CALL TO ORDER: 08084422151

Ganyen Doddoya (scent leave)

  • In Stock

  • 0 Review(s)

Price :

₦2,000

Play Video

Size :

  • M
  • L
  • XL

Estimated Shipping Time: 1-3 Days

Product SKU: jCx82274NE

Amfanin ganyen Doddoya(scent leave)
(1)Yana narkan da abinci
(2)Yana tsare mutum daga kamuwa da ciwon zuciya.
(3)Yana rage tasirin Ciwon suga (diabetes)
(4)Yana rage radadin ciwo
(5)Yana kashe bacteria da germs(qwayoyin cuta)
(6)Yana rage nikotin(nicotine)
(7)Yana tasirin wajen sanyi mai kama qabobi
(8)Yana Amafani wajen mace mai Neman haihuwa Yana wanke mahaifa(boost fertility)
(9)Yana maganin sauro(fight mosquito)
(10)Yana taimakawa wajen mura da tari
--------------------------------------------------------------------------
(1) Yadda ake amfani da dodoya wajen narkar da abinci ana hadata da lemon grass adafa ariqa sha.
(2) Yadda ake Amfani da dodoya wajen magance kamuwa da ciwon zuciya zai ariqa dafata da danyen citta anasha kaman tea
(3)Yadda aka amfani da dodoya wajen ciwon suga diabetes Asami ganyen garahuni sai ahadasu adafa ariqasha Kofi daya da safe kafin aci abinci Kofi daya da yamma har sati 3
(4) Yadda ake amfani da dodoya wajen rage radadin ciwo Asami garin kanunfari Rabin cokali ahada da ganyen dodoya adafa ariqa sha
(5)Yadda ake amfani da dodoya wajen riga kafi kamuwa da cutar bacteria zaa sameta sai ariqa sawa cikin abinci ana dafawa.
(6)Yadda ake amfani daita wajen rage nicotine wannan yafi amfani ga mai shan taba ko mai cin goro ' ajajjagata ko ayi blending dinta tare da citta danye guda daya da bayan angama sai azuba zuma aciki asha.
(7)Yadda ake amfani da dodoya wajen sanyi mai kama gabobi zaa sami dodoya da citta danye da lemun tsami da tafarnuwa da saiwar sanya sai adafa ariqa sha
(8)Yadda ake amfani dashi wajen mace mai Neman haihuwa Yana wanke dattin mahaifa zata sami dodoya da ganyen magarya ta dafa tariqasha " kuma anaso duk abincin dazata dafa ta tabbatar da tasa ganyen dodoya aciki.
(9)Yadda ake amfani da dodoya wajen maganin sauro idan akayi hayaqinta yana Koran sauro
(10)Yadda ake amfani da dodoya wajen maganin mura ana samun ganyen dodoya da citta danye sai adafa ariqa zuba Zuma anasha


Ratings & Reviews

0.0

No Review Found.


To Review


To Comment


Sold By

Boo2mall

4

Total Item

Seller's Products